Isa ga babban shafi
Wasanni

Genoa ta dakile yunkurin Juventus na kafa tarihi a Seria A

Genoa ta lallasa Juventus da kwallaye 2-0 a gasar Seria A ta kasar Italiya, abinda kawo karshen jerin wasannin da Juventus ke bugawa ba tare da shan kaye ba a gasar.

'Yan wasan Juventus bayan kammala wasan da Genoa ta doke su da 2-0.
'Yan wasan Juventus bayan kammala wasan da Genoa ta doke su da 2-0. Reuters
Talla

Yayin wasan na jiya, kocin Juventus Massmilano Allegri, ya hutar da dan wasansa Cristiano Ronaldo, wanda ya ciwa kungiyar dukkanin kwallaye uku da ta lallasa Atletico Madrid a gasar Zakarun Nahiyar Turai, matakin da wasu magoya bayan Juventus ke ganin ya taka rawa wajen kayen da suka sha a hannun Genoa.

Dan wasan Genoa Stefano Sturaro ne ya jefa kwallon farko ragar Juventus a mintuna na 72, yayinda Goran Pandev ya kara kwallo ta biyu yayinda ya rage mintuna 9 a tashi daga wasa.

Juventus ke jagorantar gasar ta Seria A da maki 75, Napoli a matsayi na 2 da maki 60, sai ta uku Inter Milan da maki 53, yayinda AC Milan ke matsayi na 4 da maki 51.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.