Isa ga babban shafi
Wasanni

Hazard ya musanta rahoton kulla yarjejeniya da Real Madrid

Dan wasan Chelsea Eden Hazard yayi watsi da rahotannin da ke cewa ya kammala cimma yarjejeniya tsakaninsa da Real Madrid dangane da komawa buga mata wasanni a karshen kakar wasa ta bana.

Dan wasan Chelsea Eden Hazard.
Dan wasan Chelsea Eden Hazard. Reuters/Eddie Keogh
Talla

Kalaman na Hazard, martani ne kan rahoton da wasu kafafen yada labarai a Spain suka rawaito, da ke cewa ya amince da yarjejeniyar komawa real Madrid inda zai shafe shekaru 5 tare da ita.

Zalika rahoton ya kara da cewa a karkashin yarjejeniyar kungiyar ta Real Madrid ta amince za ta fifita albashinsa fiye da dukkanin ‘yan wasanta.

A cewar kafafen yada labaran na Spain, sake karbar jagorancin horar da Real Madrid da Zinaden Zidane yayi ne ya karfafawa Hazard aniyar komawa kungiyar.

An dai dade ana alakanta dan wasan da sauyin sheka da Chelsea zuwa Madrid a bayan, sai dai har yanzu labarin bai tabbata ba, ko da yake shi kansa eden Hazard ya sha bayyana sha’awar bugawa kungiyar ta Real Madrid wasanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.