Isa ga babban shafi
Wasanni

United za ta ninkawa Rashford albashinsa Rashford sau 3

Manchester United za ta ninka albashin fam dubu 75 a mako daya, da ta ke baiwa dan wasanta Marcus Rashford har sau uku, a kakar wasa mai zuwa.

Mai horas da Manchester United Ole Gunnar Solskjaer tare da Marcus Rashford.
Mai horas da Manchester United Ole Gunnar Solskjaer tare da Marcus Rashford. REUTERS/Andrew Yates
Talla

Jaridar Daily Star da ke Ingila ta rawaito cewa United ta yanke shawarar ce, domin hana matashin dan wasan nata amsa tayin komawa daya daga cikin manyan kungiyoyin nahiyar Turai guda 2 da ke gasar La Liga.

Tun bayan da Manchester United ta gaza kai bantenta na samun tikitin halartar gasar Zakarun Turai ta badi, majiyoyi masu karfi ke rawaito cewa, Rashford zai iya komawa Barcelona ko Real Madrid, da zarar an bude kasuwar sauyen shekar ‘yan wasa.

Rahotanni sun ce ko a karshen makon nan, Rashford ya dakatar da tattaunawar da ke gudana tsakaninsa da shugabannin Manchester United kan kara wa’adin yarjejeniyar da ke tsakaninsu, domin nazari kan makomar kungiyar a karkashin jagorancin kocinta Ole Gunnar Solskjaer.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.