Isa ga babban shafi
Wasanni

Najeriya da Kamaru sun kai zagayen gaba a gasar kofin duniya

Kasashen Najeriya da Kamaru sun samu gurabe a zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya ta mata da ke gudana a Faransa kuma a karon farko kenan a tarihin gasar da kasashen Afrika guda biyu ke tsallakawa zuwa wannan mataki na kasashe 16 da za su ci gaba da karawa da juna.

Ajara Nchout wadda ta ci wa Kamaru kwallaye biyu a wasansu da New Zealand
Ajara Nchout wadda ta ci wa Kamaru kwallaye biyu a wasansu da New Zealand REUTERS/Jean-Paul Pelissier
Talla

Kasar Kamaru ta samu gurbinta ne bayan ta samu nasarar doke New Zealand da kwallaye 2-1 a ranar Alhamis, kwallayen da Ajara Nchout ta ci wa Kamarun.

Ita kuwa Super Falcons ta Najeriya ta kai matakin ne bayan kasar Chile ta gaza doke Thailand da kwallaye 3-0, inda ta samu nasara akan Thailand din da ci 2-0, abinda ya sa Najeriyar ta samu gurbin.

Yanzu haka Najeriya za ta hadu da Jamus a gobe Asabar, yayinda Kamaru za ta hadu da Ingila a ranar Lahadi.

A karon farko kenan cikin shekaru 20 da Najeriya ke kai wa matakin zagaye na biyu na gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.