Isa ga babban shafi
Wasanni

CONMEBOL na nazarin haramtawa Messi wasa tsawon shekaru 2

Tauraron kwallon kafar Argentina na Barcelona, Lionel Messi na fuskantar yiwuwar yanke masa hukuncin bugawa kasarsa wasa tsawon shekaru biyu, sakamakon furucinsa kan sahihancin gasar cin kofin nahiyar Kudancin Amurka ‘Copa America’.

Lionel Messi, yayinda alkalin wasa ya bashi jan kati a gasar Copa America.
Lionel Messi, yayinda alkalin wasa ya bashi jan kati a gasar Copa America. Reuters
Talla

Messi da aka baiwa jan kati yayin wasan neman gurbin na uku da suka doke Chile da 2-1, ya yi zargin cewa, an shirya sakamakon gasar ta Copa America ne domin baiwa Brazil mai masaukin baki damar lashe kofin na bana, da hadin bakin masu shirya gasar da alkalan wasa.

Idan har hukumar kwallon nahiyar kudancin Amurka CONMEBOL ta yankewa Messi hukunci, hakan na nufin dan wasan ba zai buga wasannin neman cancantar zuwa gasar cin kofin duniya ta 2022 a Qatar ba, zalika ba zai buga gasar Cope America da Argentina da Colombia za su karbi bakunci ba a shekara mai kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.