Isa ga babban shafi
Wasanni

Magoya bayan PSG sun jawo mata biyan tara

Hukumar shiryawa da kuma lura da gasar Ligue 1 ta Faransa LFP, ta ci tarar kungiyar PSG euro 2,000, saboda yadda magoya bayanta suka rika zagi da furta sauran kalamai na batanci kan Neymar, yayin wasan da suka doke Nimes.

Wani sashin magoya bayan kungiyar PSG yayinda suke furta kalaman nuna kiyayya ga Neymar.
Wani sashin magoya bayan kungiyar PSG yayinda suke furta kalaman nuna kiyayya ga Neymar. FRANCK FIFE / AFP
Talla

Nuna zazzafar adawar da magoya bayan PSG suka yi ga Neymar ya auku ne a ranar 11 gawatan Agustan da muke ciki, lokacin da suka samu nasarar doke Nimes da kwallaye 3-0.

An samu tsamin dagantaka tsakanin Neymar da magoya bayan PSG ne tun bayan da dan wasan ya fito karara ya bayyana aniyar komawatsohuwar kungiyarsa ta Barcelona, lamarin da ya kai ga Neymar din ya kauracewa yin atasaye tare da tawagar kungiyar tasata PSG yayin wasannin sharara fagen soma kakar wasa ta bana.

Har yanzu dai dan wasan bai buga PSG wasa a kaka ta bana ba, lamarin dake da alaka, da shirin komawarsa Barcelona Ko Real Madrid a kowane lokaci daga yanzu, kafin rufe hada-adarsauyin shekar ‘yan wasa a ranar 2 gawatan Satumba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.