Isa ga babban shafi
Wasanni

Makaho ya sadaukar da kudin maganinsa ga kwallo

Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Africain ta Tunisia sun hada kudin da ya kai Dala dubu 450 a cikin kwana guda domin ceto kungiyar daga matsalar kudi. Daga cikin magoya bayan har da wani makaho da ya sadaukar da kudin da ya dade yana tarawa domin yi wa kansa magani.

Wasu daga cikin magoya bayan Club Africain
Wasu daga cikin magoya bayan Club Africain kapitalis
Talla

Kungiyar Africain da aka kafa a shekarar 1920, ita ce ta biyu mafi tsufa a Tunisia , sannan tana daga cikin zaratan kungiyoyin da suka yi fice Afrika , yayin da aka cire mata maki shida, kana aka ci tarar ta saboda gazawarta wajen biyan albashin tsoffin ‘yan wasanta.

A gefe guda, Hukumar Kwallon Kafa ta Tunisia ta kafa wani kwamitin kwararru domin ceto kungiyar daga kangin da ta tsinci kanta a ciki.

A cikin watan Oktoban da ya gabata ne, Hukumar Kwallon Kafar Kasar ta kafa wani asusun banki domin magoya bayan kungiyar su zuba gudunmawarsu ta ceto ta  daga kangin bashin, kuma a lhalin yanzu an tara Dala dubu 600 na Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.