Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Barcelona ta yi kane - kane a saman teburin La Liga

Barcelona ta tafi gajeren hutun karshen shekara a saman teburin La Ligar Spain bayan ta gwada bajintar ta a kan Alaves a Asabar din nan, inda ta lallasa ta 4-1.

'Yan wasan Barcelona yayin murnar kwallon da Messi ya ci.
'Yan wasan Barcelona yayin murnar kwallon da Messi ya ci. REUTERS/Albert Gea
Talla

Real Madrid, wacce ta tashi canjaras da Barcelonan a wasan hamayya na Clasico, tana iya zuwa daidai da mai rike da kofin La Ligar kan maki 39 idan ta doke Atletico Bilbao a ranar Lahadi, amma Barcelona za ta shiga gaban ta da yawan kwallaye.

Seville na da tabbacin kasancewa ta 3 da maki 34 har a gama hutun Kiristimeti, sakamakon lallasa Mallorca da ta yi 2-0 har gida.

A wasan da Barcelona ta fafata da Alaves, dan wasan Faransa, Antoine Griezzman ne ya fara saka kwallo a raga bayan Messi ya taimaka mai a minti na 14.

Na’urar da ke taimaka wa alkalin wasa ta soke kwallon da Messi ya ci, daga nan ne kuma dan wasan Chile Arturo Vidal ya ci wa Barcelona kwallo ta 2.

Dan wasan Alaves, Pere Pons ya ci mata kwallo a minti na 56, lokacin da ‘yan wasan bayan Barcelona Gerrad Pique da Samuel Umtiti suka yi likimo.

Duk da masu tsaron baya 4 da ke biye da shi, Messi bai yi kasa a gwiwa ba a minti na 69, inda ya narka wata kwallo da kafarsa ta hagu a ragar Alaves a wajen da’ira ta 18, lamarin da ya bayyana daliln da ya sa aka ba shi kyautar gwarzon dan kwallon kafar duniya ta Ballon d ‘Or.

A minti na 75, Luis Suarez ya saka kwallo ta 4 a bugun daga – kai – sai – mai – tsaron – raga, kuma haka wasa ya tashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.