Isa ga babban shafi
Wasanni

Sadio Mane ya cire wa Liverpool kitse a wuta

Kocin Liverpool Jurgen Kloop ya ce, bai zaci ‘yan wasansa za su zabura ba a fafutukarsu ta neman lashe kofin gasar firimiyar Ingila bayan da suka yi nasarar doke West Ham da ci 3-2.

Da kyar Liverpool ta sha a hannun West Ham
Da kyar Liverpool ta sha a hannun West Ham Chris Radburn/Reuters
Talla

Yanzu haka kungiyar na bukatar lashe wasanni hudu kafin daukar kofin firimiyar Ingila a bana.

Liverpool ta kafa makamancin tarihin da Manchester City ta kafa na buga wasanni 18 a firimiya ba tare da shan kashi ba.

A 2017 ne, Manchester City ta kafa wannan tarihin tsakanin watan Agusta zuwa Disamba.

Tun watan Oktoban bara, raban da Liverpool ta raba maki da wata kungiya, lokacin da ta yi canjarsa 1-1 da Manchester United.

Sadio Mane ne ya kare Liverpool daga tashi wasan 2-2 tsakaninsu da West Ham a jiya, inda ya zura kwallo ta uku ana saura minti tara a tashi wasa, abin da ya ba ta damar bada tazarar maki 22 a teburin gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.