Isa ga babban shafi
Wasanni

PSG ta kafa tarihin zuwa wasan karshe na zakarun Turai

Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta zama ta farko daga Faransa da ta samu gurbi a wasan karshe na gasar zakarun Turai tun bayan Monaco wadda ta kai wannan matakin a shekarar 2004.

'Yan wasan PSG na murnar zura kwallo a ragar RB Leipzig ta Jamus
'Yan wasan PSG na murnar zura kwallo a ragar RB Leipzig ta Jamus Reuters
Talla

PSG ta kai wasan karshen ne bayan ta samu nasarar lallasa RB Leipzig da kwallaye 3-0 a karawar da suka yi a daren jiya a wasan dab da na karshe.

Kocin RB Leipzig Julian Nagelsmann ya amince cewa, PSG ta fi karfinsu bayan karawar da suka yi a Lisbon, yana mai bayyana takaicinsa kan yadda ‘yan wasansa suka barar da damarsu ta zura kwallaye.

RB Leipzig dai, karamar kungiya ce da aka samar da ita a shekarar 2009.

A bangare guda, gwarzon dan wasan PSG, Kylian Mbappe ya ce, yana fatar Lyon za ta doke Bayern Munich a wasan da kungiyoyin biyu za su yi yau a matakin wasan dab da na karshe na gasar ta zakarun Turai, abin da zai bai wa kungiyoyi biyu daga Faransa damar fafatawa da juna a wasan karshe na gasar.

Kodayake Mbappe ya ce, karawar da za a yi tsakanin Bayern Munich da Lyon za ta kasance zazzafa, amma a cewarsa, idan ma Bayern Munich din ce za su hadu da ita a wasan karshe, hakan ma ya yi. Sai dai ya fi son Lyon lura da cewa ita ma kungiya ce daga Faransa.

Masharhanta na cewa, mawuyaci ne PSG ta lashe kofin gasar ta zakarun Turai muddin ta hadu da Bayern Munich a wasan karshe, amma za ta iya dage kofin idan ta hadu da Lyon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.