Isa ga babban shafi
Wasanni-Coronavirus

Bundesliga ta baiwa magoya baya damar komawa kallon wasanni kai tsaye

Hukumar kwallon kafar Jamus ta baiwa kungiyoyin kwallon kafar kasar damar kyale magoya bayansu halartar filayen wasanninsu domin baiwa idanunsu abinci kai tsaye a sabuwar kakar wasa ta 2020/2021, amma karkashin tsauraron dokokin dakile yaduwar annobar coronavirus, cikinsu har da bada tazara.

Kofin gasar Bundesliga ta kasar Jamus
Kofin gasar Bundesliga ta kasar Jamus REUTERS/Michael Dalder/File Photo
Talla

Yayin sanar da basu damar hukumar kwallon kafar ta Jamus tace kashi 20 cikin 100 ne kawai na yawan magoya bayan da filayen wasanni za su iya dauke ke da damar shiga kallon wasannin kai tsaye.

A gobe Juma’a za a soma sabuwar kakar wasa ta Bundesliga a kasar ta Jamus, inda ake sa ran magoya bayan kungiyar Borussia Dortmund akalla dubu 10 kai tsaye za su kalli wasan da za ta fafata da takwararta ta Borussia Monchengladbach a gida.

A watan Mayun wannan shekara aka cigaba da fafata wasannin kakar tamaular da ta kare, bayan shafe sama da watanni 3 suna hutun dole, sai dai an cigaba da wasannin ne ba tare da ‘yan kallo ba, saboda annobar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.