Za a sake yi wa Osimhen gwajin Korona
Kungiyar kwallon kafa ta Napoli ta tabbatar da cewa za a sake yi wa dan wasanta, Victor Osimhen gwajin cutar coronavirus, saboda har yanzu cutar ba ta rabu da shi ba.
Wallafawa ranar:
Gwanji ya tabbatar dan shekarau 22 din ya harbu da cutar covid 19 ne jim kadan bayan dawowarsa daga kasarsa, Najeriya, inda ya je hutun Kiristimeti.
An yi zargin cewa dan wasan ya kamu da wannan cuta ne sakamakon yin watsi da ka’idojin da aka gindaya don dakile ta, a yayin da ya yi bikin tunawa da ranar haihuwarsa a 29 ga watan Disamba, lamarin da ya nemi afuwa a kai.
Dan wasan tawagar kwallon kafar Najeriyar ya kebe kansa na tsawon kwanaki 14, amma bayan an sake gwada shi sai aka ga burbushin cutar a tattare da shi.
A shafinta na Twitter, kungiyar Napoli ta nanata cewa za a sake yi wa dan wasan gwajin Covid 19.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu