Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

EFL za ta hukunta kungiyoyi kan yadda 'yan wasa ke karya dokokin corona

Shugaban hukumar kwallon kafar Ingila, Trevor Birch ya yi barazanar fara dakatar da ‘yan wasa daga dokawa kungiyoyinsu wasanni matukar suka ci gaba da karya ka’idojin dakile yaduwar coronavirus.

A baya bayan nan 'yan wasa da dama ne suka harbu da coronavirus wanda EFL ke alakantawa da rashin mutunta dokokin kariya daga cutar da wasu ke yi.
A baya bayan nan 'yan wasa da dama ne suka harbu da coronavirus wanda EFL ke alakantawa da rashin mutunta dokokin kariya daga cutar da wasu ke yi. Emilio Andreoli/Pool via Reuters
Talla

Gargadin Birch na zuwa dai dai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar adadin ‘yan kwallon da ke kamuwa da Covid-19 a baya baya nan.

Duk da sabbin matakan dakile walwalar jama’a a Birtaniya dai, hukumar kwallon kafar kasar ba ta amince da dakatar da wasanni ba, kamar yadda aka yi a 2020, sai dai shugaban hukumar ta EFL ya ce akwai tarin ‘yan wasa da ke kin mutunta tanade-tanaden dokar da aka gindaya don hana yaduwar cutar tsakanin ‘yan kwallo.

A baya-bayan nan dai adadi mai yawa na 'yan kwallo da masu horarwa sun harbu da cutar ta Coronavirus.

Wata wasika ta Trevor Birtch ya aikewa manajojin kungiyoyin kwallon kafar na Birtaniya ya gargadesu kan kin mutunta dokokin dai dai lokacin da wasannin zagaye na 4 na cin kofin FA ke karatowa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.