Isa ga babban shafi
Wasanni

Liverpool na fatan karkare kakar Firimiya cikin 'yan hudun saman Teburi

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce fatan tawagarsa a yanzu ba wai lashe gasar Firimiya ba ne, su na kokari ne wajen iya karkare kakar wasan bana a jerin ‘yan hudun saman teburi don samun zarafin iya zuwa gasar cin kofin zakarun Turai a kaka mai zuwa.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp. Reuters
Talla

Klopp da ke tsokaci kan rashin kokarin da tawagar ta Liverpool ke yi a baya-bayan nan musamman bayan canjaras dinsu da Manchester United a Lahadin da ta gabata, ya ce sun kammala saduda da iya lashe kofin Firimiya na bana.

Yanzu haka Liverpool ke matsayin ta 4 a teburin gasar bayan canjaras dinta da Manchester United, a bangare guda nasarar Leicester da Manchester City wadanda ke matsayin na 2 da na 3 wadanda su ka sake dagula mata lissafi.

Liverpool wadda ta faro wasannin kakar na bana da karsashi, ta fada matsala ne bayan raunin manyan ‘yan wasanta ciki har da mai tsaron bayanta Virgil van Dijk baya ga Diogo Jota a baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.