Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Mikel Arteta na fuskantar barazanar magoya bayan Arsenal

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta, ya bi sahun masu horarwa wajen kiraye-kirayen daukar mataki kan kafofin sada zumunta da nufin kawo karshen cin zarafi ko kuma nuna wariyar da ‘yan wasa ke fuskanta, kiran da ke zuwa bayan Kocin ya fuskanci barazana kan iyalansa a baya-bayan nan.

Kocin Arsenal Mikel Arteta
Kocin Arsenal Mikel Arteta REUTERS/Eddie Keogh
Talla

Arteta dan Spain ya ce yanzu haka amfani da shafinsa na Twitter ya gagareshi saboda fargabar barazanar da ake masa, inda ya ce wajibi ne kamfanonin da ke kula da shafukan su dauki matakan gaggawa la’akari da yadda hakan ke shafar harkokin wasanni a Ingila.

Ko a baya-bayan nan sai da hukumar wasanni ta Birtaniya ta aikewa da kamfanonin sada zumuntar bukatar daukar tsauraran mataki kan masu amfani da fagen wajen nuna wariya, batanci ko kuma barazanar cin zarafi kan ‘yan wasa da masu horarwa har ma da alkalan wasa.

‘yan wasa irinsu Marcus Rashford na Manchester United da Axel Tuanzebe baya ga Anthony Martial da kuma Lauren James ta tawagar mata da Romaine Sawyers da kuma Reece James, na cikin wadanda suka fuskanci kalaman wariya ta shafukan Intanet a baya-bayan nan.

A bangare guda mai horar da kungiyar Newcastle Steve Bruce ya ce ko a makwan nan sai da ya fuskanci kalaman barazana tare da yi masa fatan mutuwa, yayinda alkalin wasa Mike Dean ya janye daga alkalanci a wasannin gobe da jibi bayan barazanar kisar da ya fuskanta daga magoya bayan kwallo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.