Isa ga babban shafi
Wasanni

'Yan wasan Liverpool 3 sun murmure daga jinyar rauni

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta sanar da murmurewar wasu daga cikin ‘yan wasanta da ke jinya, wanda ya haddasa mata gagarumar koma baya a wasanninta na Firimiya cikin wannan kaka.

Dan wasan Liverpool Naby Keïta.
Dan wasan Liverpool Naby Keïta. Michael Dalder/Reuters
Talla

Cikin ‘yan wasan Liverpool da aka ga kafarsu a filin atisaye yau Litinin bayan jinyar sun hada da Naby Keita wanda rabon da ya dokawa Liverpool wasa tun nasarar tawagar kan Crystal Palace da kwallaye 7 da nema cikin watan Disamba, sai kuma Divok Origi da Ben Davies wadanda rauni ya hanasu damar taka leda a wasannin karshen mako da Liverpool din ta yi rashin nasara hannun Lester City da kwallaye 3 da 1.

Sai da har yanzu Liverpool ba ta sanar da warwarewar Fabinho na Brazil ba, ko da ya ke su kansu ‘yan wasan 3 da suka murmure babu tabbacin ko za su taka leda a karawar ta gobe karkashin gasar cin kofin zakarun Turai.

Tawagar Jurgen Klopp wadda ta rasa damar shiga Jamus don karawa da RB Leipzig a zagayen farko na kungiyoyi 16 karkahsin gasar zakarun Turai, matakin da ya tilasta kungiyoyin 2 zabar Hungary don doka wasan a gobe Talata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.