Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Alaba ya bada tabbacin zai bar Bayern Munich a karshen kaka

Dan Wasan baya na kungiyar Bayern Munich, David Alaba ya bayyana aniyarsa ta ficewa daga kungiyar a karshen wannan shekara idan kwangilarsa ta kare, bayan kwashe shekaru 13 yana yi wa kungiyar wasa.

David Alaba, dan wasan Bayern Munich.
David Alaba, dan wasan Bayern Munich. AFP
Talla

Yayin ganawa da manema labarai, dan wasan mai shekaru 28 yace yana so ya yi wani abu sabo, bayan kawo karshen zaman sa a Bayern Munich a karshen wannan kaka.

A shekaru 13 da yayi a kungiyar, Alaba wanda asalin dan Najeriya ne ya lashe kofuna 26 da suka hada da na wasan Bundesliga da kofin kalubale da kofin gasar zakarun nahiyar Turai da kuma kofin kungiyoyin duniya.

Ya zuwa yanzu dan wasan bai bayyana inda yake so ya koma ba, amma kuma rahotanni sun ce kungiyoyi irin su Barcelona da Real Madrid da Manchester City na zawarcin sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.