Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Suares ya bayyana bacin ran da Barcelona ta kunsa masa

Tsohon dan wasan gaba na Barcelona Luis Suarez ya bayyana abin takaicin da ya fuskanta a tsohuwar tawagar tasa, ta yadda hukumomin kungiyar suka shaida masa cewa ya yi tsufan da ba zai iya tabuka abin kirki a matakin kololuwa na Tamaula ba.

Luis Suarez tsohon dan wasan Barcelona da ya koma taka leda da Atletico Madrid.
Luis Suarez tsohon dan wasan Barcelona da ya koma taka leda da Atletico Madrid. REUTERS
Talla

A watan Satumban bara ne Suarez ya yi hannun riga da Barcelona, a wani sauyin sheka da Lionel Messi ya bayyana a matsayin rashin tunani.

Sauya shekar ta Suares mai shekaru 34 a wancan lokaci tamkar bayyanawa tsohuwar tawagar tasa kuskurenta ne, musamman ganin yadda yanzu haka ya ke cirewa Atletico Madrid kitse a wuta cikinw asannin gasar La Liga da ta ke matsayin jagora.

Suares wanda ya ce yana ciwa Barcelona akalla kwallaye 20 kowacce kaka, ya kai kololuwar bajinta ne cikin tsohuwar tawagar tasa a kakar wasa ta 2015-16 inda ya zura kwallaye 59 fiye da wanda Messi ya zura, wanda ya bashi damar lashe takalmin zinare na nahiyar Turai.

Tsohon dan wasan da ke fama da rauni yanzu haka ya ce yana matukar jin dadain take leda da Atletico Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.