Messi da Ronaldo sun samu koma baya a jerin wadanda za su lashe Balon d'Or
Shahararrun ‘yan wasan kwallon kafa, Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da Neymar sun samu koma baya a jerin ‘yan wasan da ake sa ran za su lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya ta Balon d’Or ta shekarar 2021.
Wallafawa ranar:
Messi wanda shi ke rike da kambun, kuma sau 6 yana lashe kyautar yana matsayi na 3 a cikin jerin ‘yan wasa 20 da aka fitar, yayin da Cristiano Ronaldo, wanda sau 5 ya ci kyautar yana matsayi na 8 sai Karim Bnezema a matsayi na 9.
Neymar Junior yana matsayi na 19, Luka Modric na matsayi na 15, Luiz Suarez na lamba 13.
Robert Lewandowky, dan wasan Bayern Munich yana matsayi na 1, sai Kylian Mbappe na PSG da Faransa na a matsayi na 2.
A watan Disamba ne za bayyana wanda ya lashe kyautar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu