UEFA ta baiwa birnin Rome damar karbar bakuncin gasar Euro 2020
Hukumar kwallon kafa ta Turai UEFA ta tabbatar da birnin Rome a matsayin wanda zai karbi bakuncin gasar cin kofin kasashen Turai ta Euro 2020, wadda aka sauya lokacinta na gudana daga shekarar ta bara zuwa bana saboda annobar Korona.
Wallafawa ranar:
Jadawalin gasar cin kofin kasashen Turan dai ya nuna cewar, birnin na Rome ne zai karbi bakuncin wasannin farko da za su gudana a gasar da hadin gwiwar kasashen Turkiya da Italiya za su karbi bakunci.
A nasu bangaren kuma hukumomin kasar Italiya sun bada tabbacin cewar za a baiwa ‘yan kallo damar baiwa idanunsu abinci kai tsaye yayin wasannin da za su gudana a babban filin wasan birnin na Rome.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu