Isa ga babban shafi
UEFA-ESL

UEFA za ta sanar da makomar kungiyoyin da suka amince da Super League

Yau juma’a hukumar UEFA ke shirin gudanar da taro na musamman don sanar da matakin da za ta dauka kan kungiyoyin Turai 12 da suka amince da tayin gasar European Super League a baya-bayan, duk da ya ke 9 daga cikinsu sun sanar da janyewa biyo bayan barazanar hukumar da kuma boren magoya baya da su kansu ‘yan wasan

Shugaban hukumar UEFA, Aleksander Ceferin.
Shugaban hukumar UEFA, Aleksander Ceferin. Richard Juilliart UEFA/AFP/Archives
Talla

Sai dai dai dai lokacin da UEFA ke shirin wannan taro shugaban kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Florentino Perez ya yi ikirarin cewa ficewar kungiyoyi 9 daga cikin 12 da suka amince da gasar tun da farko, ba shi ke nuna an jingine maganar gasar ta Super League a gefe ba.

Perez wanda ke cikin 'yan gaba gaba da ke goyon bayan gasar ta ESL har zuwa yanzu bai sanar da janye kungiyarsa ba duk da boren magoya baya da kuma barazanar hukumar kwallon kafar ta Turai, inda a jawabinsa ya bayyana cewa gasar ba ta mutu ba.

Shugabancin kungiyoyi da dama ne dai ke ci gaba da kiraye-kiraye ga UEFA don ta dauki matakin ladabtarwa ga kungiyoyin 12 da suka amince da gasar ta ESL.

Haka zalika shugaban hukumar ta UEFA Aleksander Ceferin ya sanar da yiwuwar bayyana sunayen biranen da za su karbi bakoncin gasar Euro 2020 da coronavirus ta tilasta dagewa zuwa bana.

Kawo yanzu dai birane 9 daga cikin 12 da za su karbi bakoncin gasar sun amince da bukatar UEFA na baiwa ‘yan kallo damar shiga filayen wasa, yayin wasannin gasar tsakanin 11 ga watan Yuni zuwa 11 ga watan Yuli.

Sai dai har yanzu akwai tantama kan biranen Bilbao Dublin da kuma Munich wadanda basu kamala tsayar da ko za su amince da bukatar ta UEFA ba, ko da Aleksander Ceferin tun a yammacin jiya ya sanar da cewa za a dauke wasannin gasar daga birnin Bilbao.Sauran biranen da suka amince da baiwa kasha 25 na ‘yan kallo damar shiga filayen wasanni yayin gasar ta EURO sun kunshi, Budapest da St Petersburg da Baku da Amsterdam da Bucharest da Glasgow da kuma Copenhagen baya ga Rome da London.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.