Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Hazard zai yi kokarin nuna bajintarsa kan Chelsea- Thomas Tuchel

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Thomas Tuchel ya amsa cewa tabbas tsohon dan wasan tawagar da ke taka leda da Real Madrid, Eden Hazard zai yi kokarin nuna bajinta wajen samarwa tawagarsa maki a karawar kungiyoyin biyu karkashin gasar zakarun turai.

Chelsea manager Thomas Tuchel
Chelsea manager Thomas Tuchel John Walton POOL/AFP
Talla

Hazard dan Belgium wanda ya rika fama da jinyar raunin tun bayan sauya shekarsa zuwa Spain a 2019 kan yuro miliyan 89, har kawo yanzu kwallaye 4 kacal ya iya zurawa sabuwar kungiyar tasa Real Madrid cikin dukkanin wasannin da ya doka mata.

Sai dai a baya-bayan nan ne dan wasan ya dawo daga jinya kuma yana daga cikin wadanda za su taka leda a karawar ta yau, wanda Tuchel ke cewa akwai yiwuwar ya yi iyakar kokarinsa wajen nuna bajinta kan tsohon club din nasa.

A cewar Tuchel Hazard gogaggen dan wasa ne kuma haziki, wanda har yanzu su na bashi dukkanin girmamawar da ta kamata haka zalika basa manta irin gagarumar gudunmawar da ya bai wa Chelsea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.