Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Facebook zai dauki mataki kan kalaman wariyar da aka yiwa Sterling

Dan wasan gaba na Manchester City Raheem Sterling ya gamu da kalaman nuna wariya sa’o’i kalilan bayan kungiyoyin Firimiya sun kawo karshen kauracewa shafukan sada zumunta da suka yi na sa’o’i 48.

Manchester City forward Raheem Sterling
Manchester City forward Raheem Sterling CARL RECINE POOL/AFP
Talla

Kalaman nuna wariyar kan Sterling ya biyo bayan nasarar City kan PSG a gasar cin kofin zakarun Turai wanda ya bai wa kungiyar damar kai wa wasan karshe da za ta kara da Chelsea a gasar.

Tuni dai Facebook wanda shi ke da Instagram ya yi tsokaci kan batun inda kakakinsa ke cewa cin zarafin ga Sterling ba abin yarda ba ne kuma Istagram ba zai ci gaba da amincewa da irinsu ba.

A cewar kakakin na Facebook da kuma Istagram, kamfanin zai dauki mataki kan shafin da ya wallafa kalaman nuna wariyar.

A cewarsa duk da ya ke ba za su iya kawo karshen matsalar dare guda ba, amma za su yi dukkan mai yiwuwa wajen maganceta sannu a hankali.

Za a iya cewa matakin kungiyoyin na kauracewa shafukan sada zumunta ya yi aiki matuka la’akari da yadda cikin sauri kamfanin ya sha alwashin daukar mataki sabanin a baya da ya ke yin mindikis ko da anci zarafin ‘yan wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.