Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Bayern Munich ta lashe Bundesliga a karo na 9 a jere

Bayern Munich ta sake lashe gasar Bundesliga ta bana a karo na 9 a jere sakamakon nasarar da kungiyar Borussia Dortmund ta samu 3-2 a kan kungiyar RB Leipzig, wadda ke matsayi na biyu a tebur.

Wasu 'yan wasan Bayern Munich.
Wasu 'yan wasan Bayern Munich. ANDREAS GEBERT POOL/AFP
Talla

Wannan nasarar ta Dortmund ta kawar da duk wata fatar kama kungiyar Bayern Munich wadda ke matsayi na farko da maki 71 kafin karawar da za ta yi yau Asabar, yayin da Leipzig ke da maki 64 da sauran wasanni 6.

Nasarar ta yau ta kawo adadin lashe gasar Bundesliga da Bayern Munich ta yi zuwa 31 kuma yanzu haka sau 9 kenan tana daukar kofin a jere kowacce shekara tun daga shekarar 2013.

Daga cikin nasarorin da kungiyar ta samu a wasan gida har da lashe kofin kalubale sau 20 da lashe kofin zakaran zakaru na cikin gida sau 8.

A gasar cin kofin zakarun Turai kuwa, sau 6 kungiyar ke lashe kofin, yayin da ta lashe Europa sau guda a shekarar 1996, sai kuma kofin zakaran zakaru na Turai sau biyu a shekarar 2013 da 2020.

Bayern ta kuma lashe kofin duniya na kungiyoyi sau biyu a shekarar 2013 da 2021 sai kuma kofin kungiyoyi na nahiyoyi sau biyu a shekarar 1977 da 2001.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.