Isa ga babban shafi
Wasanni - Kwallon Kafa

Oshoala ta zama 'yar Afrika ta farko da ta lashe gasar zakarun Turai

Asisat Oshoala ta kafa tarihin zama ‘yar Afrika kuma ‘yar Najeriya mace ta farko da ta lashe kofin gasar Zakarun Turai ajin mata.

Tauraruwar kungiyar Barcelona, Azizat Oshoala
Tauraruwar kungiyar Barcelona, Azizat Oshoala AP - Gabriel Bouys
Talla

Shahararriyar ‘yar wasan mai shekaru 26, ta shiga wasan karshen da suka fafata da Chelsea a gasar Zakarun Turan ne a mintuna na 71, wasan da daga karshe suka lallasa kungiyar ta Chelsea da kwallaye 4-0.

Tawagar Barcelonan ajin mata ta samu nasarar ce ta hannun ‘yan wasanta Melanie Leupolz, Aleia Puttellas, Aitana Bonmati da Caroline Graham, yayin da ‘yar Najeriya Azizat Oshoala ta jefa ta biyar amma alkali ya soke ta bisa hujjar tayi satar shiga fage.

Kafin nasarar bana, yunkurin karshe da Barcelona ta yi wajen lashe kofin gasar zakarun Turan ajin mata, shi ne wasan da Lyon ta lallasa ta da kwallaye 4-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.