Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Suarez ya kara ratar da ke tsakanin Atletico da Real Madrid a La Liga

Kwallon Luis Suarez a minti na 83 gab da tashi daga wasa ya taimakawa Atletico Madrid ci gaba da jan zarenta matsayin jagora a teburin La Liga dai dai lokacin da ake gab da kammala gasar ta bana, inda suka tashi wasa a karawar tsakaninsu da Osasuna da kwallo 2 da 1.

Luis Suarez na Atletico Madrid.
Luis Suarez na Atletico Madrid. PIERRE-PHILIPPE MARCOU AFP/Archives
Talla

Idan har da Atleticon ta yi rashin nasara ko kuma canjaras a karawar ta jiya kai tsaye Real Madrid wadda ta lallasa Athletic Bilbao har gida da kwallo 1 mai ban haushi ka iya zama jagora amma kwallon ta Suarez ta hana faruwar hakan.

Atletico ce dai ta karbi bakoncin wasan amma kuma har minti na 80 da fara wasa bata iya zura kwallo ba yayinda Osasuna ke da kwallo 1 ta hannun dan wasan Ante Budimir bayan soke kwallon Stefan Savic.

Sai dai kwallon Reanan Lodi a minti na 82 da kuma Suarez a minti na 88 ya bai wa kungiyar gagarumar nasarar kara tazarar da ke tsakaninta da Real Madrid din da kuma Barcelona.

Yanzu haka dai Atletico na bukatar nasara daya ne tal a karawarta da Real Valladolid cikin makon nan, don nasarar lashe kofin na La Liga karo na 2 a shekaru 25.

Za a iya cewa Sayen Suarez wanda Barcelona ta rabu da shi cikin cin mutunci ya yiwa kungiyar rana yayinda ita kuma Barcelonar ta hakura daga tseren lashe kofin bayan rashin nasara har gida a hannun Celta Vigo da kwallo 2 da 1.

Suarez wanda ke ci gaba da nanatawa tare da kokanta cin mutuncin da Barcelona ta yi masa daya kai ga raba garinsa da ita a kakar da ta gabata, dage kofin na La Liga zai zame masa mai cike da tarihi tare da nunawa tsohuwar kungiyar tasa gazawarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.