Isa ga babban shafi
Wasanni - Falasdinawa

Pogba da Diallo sun nuna goyon baya ga Falasdinawa bayan wasan Manchester

Fitaccen 'dan wasan Faransa Paul Pogba tare da abokin taka ledar sa a kungiyar Manchester United Amad Diallo sun daga tutar Falasdinu a filin wasan Old Trafford bayan karawar da suka yi da kungiyar Fulham a daren Talata, abinda ya janyo hankalin masu bibiyan harkar kwallon kafa a duniya suna ta mahawara akai.

Dan wasan Faransa da Manchester United Paul Pogba da abokin karawarsa Amad Diallo yayin wasa da Fulham 18 ga watan Mayu 2021
Dan wasan Faransa da Manchester United Paul Pogba da abokin karawarsa Amad Diallo yayin wasa da Fulham 18 ga watan Mayu 2021 Laurence Griffiths POOL/AFP
Talla

Wani daga cikin Yan kallo ne ya mikawa Pogba tutar mai dauke da launin Ja da Fari da kuma Shudi bayan tashi daga wasan, lokacin da Yan wasan Manchester United ke zagaya fili suna yiwa magoya bayan su godiya kan irin goyan bayan da suka basu a wannan kaka mai karewa, bayan kammala wasan su na karshe a gida kamar yadda aka saba.

'Yan wasan Manchester United, ciki harda Bruno Fernandes, da Paul Pogba yayin wasa da Fulham 1 ga watan Janairu 2021
'Yan wasan Manchester United, ciki harda Bruno Fernandes, da Paul Pogba yayin wasa da Fulham 1 ga watan Janairu 2021 CARL RECINE POOL/AFP/Archives

Wannan ya sa Pogba tare da Diallo dan kasar Cote d’Ivoire wadanda dukkan su Musulmai ne suka rike tutar a gaban Yan kallo akalla 10,000 da suka halarci wasan saboda takaita Yan kallo da akayi sakamakon annobar korona.

Zanga-zangar goyon bayan Falasdinu a sassan duniya

Dubban mutane ne suka shiga zanga zanga a kasashen Turai da dama ciki harda biranen London da Berlin da madrid da kuma Paris domin bayyana goyan bayan su ga Falasdinawa sakamakon munanan hare haren da Israila ke kaiwa a Yankin Gaza wanda yayi sanadiyar hallaka mutane sama da 200.

Magoya bayan Hezbollah dauke da tutotin Falastin yayin zanga-zanga
Magoya bayan Hezbollah dauke da tutotin Falastin yayin zanga-zanga Mahmoud ZAYYAT AFP/File

Suma 'Yan wasan kungiyar Licester Hamza Choudhry da Wesley Fofana sun nuna irin wannan goyan baya a karawar da suka yi da Chelsea a wasan karshe na cin kofin FA da akayi a karshen mako wanda suka samu nasara akai.

Yahudawa sun nuna damuwa

Daukar irin wannan tuta na Falasdinu da Mohammed Elneny na kungiyar Arsenal ya yi ya gamu da suka daga Yahudawan dake goyan bayan kungiyar.

Elneny ya aike da sako ta twitter inda yake cewa, ‘zuciyar sa da ruhin sa da kuma goyan bayan sa na tare da Falasdinu’.

Kungiyar Arsenal ta shaidawa kafar talabijin na Sky Sports cewar tayi Magana da Elneny bayan da kamfanin coffee na Lavazza dake daukar nauyin kungiyar yayi korafi akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.