Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Atletico Madrid ta lashe gasar La Ligar Spain ta bana

Kungiyar Atletico Madrid ta lashe gasar La Ligar Spain ta bana sakamakon nasarar da ta samu kan kungiyar Real Valladoid a karawar da suka yi yau da ci 2-1 abin da ya bata maki 84 sama da kungiyar Real Madrid mai 82 da Barcelona mai 77.

'Yan wasan Atletico Madrid na murnar lashe La Liga.
'Yan wasan Atletico Madrid na murnar lashe La Liga. CESAR MANSO AFP
Talla

Wannan nasara ta kawo karshen makonnin da aka yi ana dakon sakamakon yadda kungiyoyin guda 3 Atletico da Real da kuma Barcelona ke tafiya tare wajen ganin wanda zai lashe kofin.

A karawar da aka yi yau Luiz Suarez da Angel Correa suka jefa wa Atletico kwallayen ta guda 2 wadanda suka taimaka mata samun nasara ta farko wajen lashe kofin tun daga shekarar 2014.

Bisa al’ada dai kungiyar Real Madrid da Barcelona ke kokawar lashe wannan kofi, kuma su suka fi sauran kungiyoyin samun nasara.

Tarihi ya nuna cewar Real Madrid ke sahun farko wajen lasje kofin da nasarori sau 34, sai Barcelona mai nasarori 26, sannan Atletico Madrid mai 11.

A karawar ta yau Real Madrid ta doke Villareal da ci 2-1, yayin da Barcelona ta doke Eibar da ci 1-0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.