Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

chelsea na iya samun kwarin gwiwa daga doke Man City -Tuchel

Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya ce tawagarsa za ta tinkari wasan karshe na gasar zakarun nahiyar Turai da za su fafata da Manchester City a karshen mako da kwarin gwiwa saboda nasarorin baya bayan nan da ta samu a kan City din.

Kocin Chelsea Thomas Tuchel.
Kocin Chelsea Thomas Tuchel. JAVIER SORIANO AFP
Talla

Chelsea da ake wa inkiya da ‘The Blues’ za su gwada kwanji da City  a birnin Porto na kasar Portugala a ranar Asabar bayan da suka kammala gasar Frimiyar Ingila a cikin jerin kungiyoyi na hudun farko duk da doke su 2-1 a gidan Aston Villa.

A wasan  kusa da karshe na gasar kofin FA  a Ingila, sai da Tuchel ya doke Guardiola a watan da ya gabata, wato ya cusa wa City rashin nasara a gida da suka dade ba su gani ba, amma daga nan dai Chelsea suka yi rashin nasara a wasanni  3 a dukkan gasani.

Dan kasar Jamus din wanda ya maye gurbin Frank Lampard  a watan Janiaru, ya ce shiga jerin kungiyoyi na gaba gaba 4 a teburin gasar Firimiyar Ingila duk da rashin nasara a Villa wata gagarumar nasara ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.