Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Tottenham na shirin yiwa tsohon Manajanta Mauricio Pochettino kiranye

Wasu bayanai na cewa, kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta fara tuntubar tsohon manajanta Mauricio Pochettino da nufin dawo da shi aikin horar da ‘yan wasanta.

Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Mauricio Pochettino, wanda ke aikin horar da PSG ta Faransa a yanzu.
Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Mauricio Pochettino, wanda ke aikin horar da PSG ta Faransa a yanzu. FRED TANNEAU AFP/Archives
Talla

Pochettino dan Argentina mai shekaru 49, a watan Nuwamban 2019 ne Tottenham ta koreshi bayan yi mata aiki na shekaru 5 matakin da ya sanya shi karbar ragamar horar da PSG a watan Janairun 2020.

Sai dai Pochettino ya gaza kai PSG ga nasarar lashe kofin lig 1 haka zalika kungiyar ta sha kaye a hannun Manchester City a wasan gab da na karshe na cin kofin zakarun Turai ko da ya ke ta dage kofin Faransa.

A bangare guda ita ma Tottenham a watan jiya ta kori Jose Mourinho wanda ta maye gurbin Pochettino da shi, yayinda da ta nada Ryan Mason aikin horar da kungiyar na wucin gadi, wanda a karkashinsa Spurs ta yi rashin nasara a wasan karshe na Carabao hannun Manchester City yayinda ta kammala wasannin Firimiya a matsayin ta 7.

Duk da Tottenham ba ta ce komi game da jita-jitar dawo da tsohon manajan na ta ba, amma yau Alhamis ta wallafa wata doguwar tattaunawar tsohon manajan inda a cikinta ya ke bayyana kyakkyawar alakar da ke tsakaninsa da kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.