Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Waye zai maye gurbin da Zidane ya bari a Real Madrid?

Hankulan masu sharhi da sauran masu bibiyar kwallon kafa sun koma kan dakon ganin zabin da kungiyar Real Madrid za ta yi na wanda zai maye gurbin kocinta Zinaden Zidane da ya yanke shawarar ajiye aikinsa a daren ranar Laraba.

Zinédine Zidane.
Zinédine Zidane. PIERRE-PHILIPPE MARCOU AFP/Archives
Talla

Zidane ya kawo karshen aikinsa ne bayan jagorantar Real Madrid wajen lashe manyan kofunan da suka hada da na gasar zakarun nahiyar Turai 3 a jere, sai kuma kofunan gasar La Liga 2.

Tsohon kocin Real Madrid Zinédine Zidane, rike da kofin gasar zakarun Turai karo 3 da ya jagoranci kungiyarsa wajen lashewa a shekarar 2018.
Tsohon kocin Real Madrid Zinédine Zidane, rike da kofin gasar zakarun Turai karo 3 da ya jagoranci kungiyarsa wajen lashewa a shekarar 2018. GENYA SAVILOV AFP/Archives

Sauran kofunan da Zidane ya lashewa Real Madrid a zamanin da ya horas da kungiyar sun hada da na gasar Spanish Super Cup 2, babbar gasar turai ta European Super Cup 2, da kuma kasar zakarun kungiyoyin duniya ta Club World Cup guda biyu.

A halin yanzu dai wadanda ake sa ran kungiyar ta Real Madrid za ta zaba don maye gurbin Zidane sun hada da tsohon kocin Juventus Massmiliano Allegri, Antonio Conte da shi ma jiya a ajiye aikinsa da Inter Milan, sai kuma Raul Gonzalas, tsohon tauraron kungiyar ta Real da a yanzu yake horas da kungiyar ta Castilla ajin matasa.

Tsohon mai horas da Juventus Massimiliano Allegri.
Tsohon mai horas da Juventus Massimiliano Allegri. AFP

Tun a shekarar 2018 ne dai aka alakanta Allegri da kulla yarjejeniya da Real Madrid lokacin da Zidane ya ajiye aikinsa a karon farko, kafin ya sake karbar ragamar jagorancin Madrid din a shekarar 2019.

Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka Inter Milan da Juventus ne neman kulla yarjejeniya da shi Allegri.

A yanzu dai lokaci ne kawai zai fayyace makomar aikin horas da Real Madrid da kuma ta masu horaswar uku da ake alakantawa da kulla yarjejeniya da kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.