Koeman zai ci gaba da jagorancin Barcelona - Laporta
Shugaban kungiyar kwallon kafar Barcelona dake kasar Spain Joan Laporta ya bayyana cewar Ronald Koeman zai cigaba da jagorancin kungiyar a kaka mai zuwa duk da korafe korafen da wasu Yan wasa da magoya bayan kungiyar ke yi.
Wallafawa ranar:
Bayan wani taron Daraktocin kungiyar da aka gudanar yau, Laporta yace sun yanke hukuncin baiwa Koeman karin damar cigaba da jagorancin kungiyar kamar yadda kwangilar shi ta nuna.
Shugaban kungiyar yace suna da yakinin cewar matakin da suka dauka na cigaba da tafiya da Manajan shine mafi alheri a gare su da Barcelona kuma suna farin ciki da haka.
Laporta yace babu tantama sun tattauna matsayin Koeman da rawar da ya taka a kakar da ta gabata kuma sun yanke hukuncin yin gyara akan wasu daga cikin matsalolin da suka fuskanta, yayin da akasarin Daraktocin suka bayyana goyan bayan cigaba da tafiya da manajan.
Shugaban kungiyar ya yaba da dattakon da manajan ya nuna kuma dama sun san shi da irin wadannan halaye na kwarewa, yayin da suke fatar ganin sun samu cigaba a kaka mai zuwa.
Rahotanni sun ce daukar Sergio Aguero daga kungiyar Manchester City na daga cikin dalilan da suka sanya tauraron kungiyar Lionel Messi sauya matsayin sa na cigaba da zama a kungiyar bayan a shekarar da ta gabata ya gabatar da takardar neman sauya sheka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu