An sassauta wa Siasia hukuncin haramcin har abada
Kotun Sauraran Kararrakin Wasanni ta rage haramcin da aka yi wa tsohon kocin tawagar Najeriya Samson Siasia na shiga harkokin wasanni har abada saboda samun sa da lafin cin hanci da rashawa a harkar wasannin.
Wallafawa ranar:
Yanzu haka a maimakon haramcin na har abada da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya ta yi masa, kotun ta rage hukuncin zuwa shekaru biyar kacal.
A cikin watan Afrilun 2019 ne, FIFA ta samu siyasa da aikata lafiin na sauya sakamakon wasa a 2010.
Kotun ta amince da hukuncin da FIFA ta yi wa Siasia, amma ta rage yawan tsawon haramcin da aka yi masa, sannan ta yi watsi da kudin da aka ci sa tara na Dala dubu 54, kwatankwacin Nairar Najeriya miliyan 21 da dubu 320.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu