Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Manchester United ta amince da farashin Jadon Sancho na Borussia Dortmund

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta amince da farashin dan wasan gaba na Borussia Dortmund Jadon Sancho, dan wasan da kungiyar ta jima ta na maitar saye amma aka gaza cimma jituwa tsakaninta da kungiyarsa a bara.

Dan wasan gaba na Ingila Jadon Sancho
Dan wasan gaba na Ingila Jadon Sancho JUSTIN TALLIS AFP
Talla

Manchester United mai doka Firimiya ta amince da biyan yuro miliyan 85 matsayin farashin dan wasan mai shekaru 21 da ya bar Manchester City a shekarar 2017.

Duk da cewa ba a kai ga cimma jituwa kan sharuddan dan wasan na Ingila na radin kai da zai kai ga gwaje-gwajen lafiya gabanin Karkare kammala sauya shekar ba, tuni bangarorin biyu suka wallafa cinikin Sancho.

Manajan Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya yi maraba da matakin sayen Sancho, wanda zai taimaka wajen bunkasa tawagar wadda ta iya kai labari wajen karkare gasar Firimiya matsayin ta 2 a teburi duk da cewa ta yi rashin nasara a wasan karshe na Europa hannun Villarreal.

Solskjaer dai na son bunkasa gaba da kuma tsakiyar United gabanin kaka mai zuwa don magance matsalar da kungiyar ke fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.