Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Ramos ya yi watsi da tayin Arsenal, City kafin ya koma PSG

Sai da Sergio Ramos ya yi watsi da tayi daga Arsenal da Manchester City kafin  ya amince da batun komawa Paris Saint-Germain.

Sergio Ramos.
Sergio Ramos. ANDER GILLENEA AFP/Archives
Talla

Dan wasan bayan ya sanya hannu a kwantirakin shekaru 2 da kungiyar ta kasar Faransa bayan da ya bar Real Madrid  a karshen kaka.

Tauraron dan wasan kasar Spain din ya  tattauna da kungiyoyi da dama amma ya yi amannar cewa tayin da Paris Saint Germnain ta yi mai gwabi ne,  wanda ba zai iya kyalewa ba.

Duk da cewa Arsenal ta bai wa Ramos kwantiragin shekaru 2 da albashin Fam miliyan 15 duk shekara, dan wasan ya yi fatali da shi saboda Arsenal ba za ta fafata a gasar zakarun nahiyar Turai ba.

City  ta wa Ramos tayin kwantiragin da zai kare a 2023, amma kuma ta ce zai je ya buga wa kungiyar New York City da ke wasa  a MLS, amma ya ce ba za ta sabu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.