Wasanni-Kwallon Kafa
Aguero zai yi zaman jinyar makwanni 10
Dan wasan gaba na Barcelona Sergio Aguero zai shafe tsawon makwanni 10 yana jinya kuma ba tare da buga kwallo ba saboda raunin da ya samu a sharabarsa kamar yadda kungiyar ta La Liga ta sanar.
Wallafawa ranar:
Talla
Barcelona ta ce, gwajin da aka yi wa dan wasan ya tabbatar da cewa, ya samu raunin.
Aguero mai shekaru 33, ya koma Barcelona ne daga Manchester City akan kwantiragin shekaru biyu.
Ya shafe shekaru 10 yana buga kwallo a Manchester City, inda ya kafa tarihin zama dan wasan da ya fi ci mata kwallaye a tarihi, domin kuwa ya daga raga har sau 260 a cikin wasanni 390.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu