Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Faransawa sun kasa, sun tsare, suna jiran Messi

Faransa cikin zumudi na ci gaba da dakon isowar Lionel Messi, inda magoya baya suka yi zaman-dirshen a harabar filin wasa na  PSG domin yin tozali da gwarzon dan wasan wanda ake sa ran zai kulla kwantiragi da kungiyar bayan ya raba gari da Barcelona.

Dimbin Magoya bayan PSG na dakon isowar Lionel Messi
Dimbin Magoya bayan PSG na dakon isowar Lionel Messi Zakaria ABDELKAFI AFP
Talla

Magoya bayan na PSG sun kasa sun tsare a kofar shiga filin wasan na Parc des Princes, suna fatan dan wasan zai bayyana a gabansu, yayin da wasunsu suka yi cincirindo a filin jiragen sama na Le Bourget domin ganin isowar Messi.

Jaridar Le Parisien ta rawaito cewa, la’alla dan wasan ya iso birnin Paris a jiya Litinin ko kuma yau Talata.

Wakilan Kamfanin Dillancin Labarai na AFP sun ce, sun ga Messi har yanzu yana nan a gidansa da ke kusa da birnin B arcelona tare da iyalansa da kuma abokinsa, Luis Suarez.

A yayin bankwanansa da Barcelona, Messi ya ce, da yiwuwar ya koma PSG
A yayin bankwanansa da Barcelona, Messi ya ce, da yiwuwar ya koma PSG Pau BARRENA AFP

A yayin bankwanansa da Barcelona bayan shafe shekaru 21 yana doka mata kwallo, Messi ya kankyasa wa jama’a cewa, da yiwuwar ya koma PSG.

Ana dai ganin cewa, PSG ce kadai kungiyar da za ta iya daukar dawainiyar biyan Messi albashin da ya kai Dala miliyan 41 a duk shekara.

Jaridar Daily Star ta rawaito cewa, da yiwuwar Manchester United na shirye-shiryen gabatar da gwaggwaban tayi domin janyo hankalin Lionel Messi har ya fasa komawa PSG.

Ita kuwa Jaridar  Athletic cewa ta yi, PSG din ta sanya ‘yan wasanta 10 a kasuwa da suka hada da Idrissa Gueye dan asalin kasar Senegal domin kammala shirinta na kulla kwantiragi da Messi.

Sai kuma Le Parisien wadda ta ce, a yanzu kam, PSG ta kawo karshen marmarinta kan dan wasan tsakiya na Manchester United, Paul Pogba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.