Kante na takarar lashe kyautar gwarzon dan wasa
‘Yan wasan Chelsea biyu da suka hada da N’Golo Kante da Jorginho na cikin jerin ‘yan wasan da Hukumar Kwallon Kafa ta Turai ta zayyana sunayansu domin zaben gwarzo shekara daga cikinsu da ya cancaci lashe kyautar hukumar a bana.
Wallafawa ranar:
Kazalika akwai Kevin De Bruyne na Manchester City a cikin masu takarar lashe kyautar gwarzon dan wasan na kakar 2020 zuwa 2021.
Kante da Jorginho sun taka gagarumar rawa a wasan da Chelsea ta doke Manchester City da cin 1-0 a birnin Porto a cikin watan Mayu, abin da ya sa Chelsea din ta lashe kofin zakarun Turai.
A ranar Alhamis mai zuwa ne za a gudanar da bikin ayyana wanda za a mika wa kyautar a birnin Santanbul na Turkiya.
Kazalika a wannan ranar ce kuma, Hukumar ta UEFA za ta fitar da sabon jadawalin gasar cin kofin kasashen Turai ta bana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu