Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Ba a sanya Giroud a tawagar kwallon kafar Faransa ba

Olivier Giroud bayab cikin ‘yan wasan tawagar Faransa da za su fafata a  wasannin neman cacantar shiga gasar cin kofin duniya na wata Satumba da Koch Didier Deschamps ya bayyana a yau Alhamis, bayan ya gayyaci wasu ‘yan wasa da ba su taba buga wa tawagar kasar wasa ba.

Olivier Giroud.
Olivier Giroud. POOL/AFP/Archives
Talla

Giroud, wanda a wata mai zuwa zai cika shekaru 35 da haihuwa a wata mai zuwa bai samu shiga wannan tawaga ba duk da cewa saura kwallaye biyar ya cimma Thierry Henry wanda ya ci wa tawagar Faransa kwallaye 51.

Dan wasan gaban ya bar Chelsea zuwa AC Milan  ta Italiya  don neman murza tamaula a kai a kai.

A Lahadin da ta gabata ya buga wa AC Milan wasa na farko, a karawa da Sampdoria a gasar Serie a.

Giroud na daya daga cikin ‘yan wasa 9 da ke cikin tawagar Faransa a gasar Euro 2020, amma kuma bai fafata a wasanninta da  Bosnia-Herzegovina da kuma Ukraine da Finland ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.