An yi wa Pele tiyata a hanjinsa
An yi nasarar yi wa shahararren tsohon dan kwallon duniyar nan, Pele tiyata a wani bangare na hanjinsa, inda aka cire masa wani kullutu da aka gano a tattare da shi.
Wallafawa ranar:
Pele mai shekaru 80 ya shafe tsawon kwanaki 6 yana kwance a asibiti, yayin da a jiya Litinin ya sanar a shafin sada zumunta cewa, an yi masa tiyatar tun a ranar Asabar da ta gabata.
An dai gano matsalar ce a tare da shi a yayin yi masa gwaje-gwajen lafiyar jikinsa da kuma bugawar zuciyarsa.
Yanzu haka yana ci gaba da murmurewa a asibitin Sao Paulo.
Tsohon dan wasan na duniya ya shafa fama da jerin cutuka a shekarun baya-bayan nan, inda a ko a shekara ta 2019 ya yi jinya a birnin Paris saboda lalurar mafutsara, yayin da kuma aka yi masa aiki a kodarsa a Brazil a 2014.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu