Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Mourinho ya cika mayar da hankali a kan abokan hamayya - Dele Alli

Dan wasan tsakiya na Tottenham, Dele Alli yace tsohon kocinsa Jose Mourinho ya cika mayar da hankali a kan abokan hamayya a yayin shirye shiryen tinkarar wasa.

Dele Alli.
Dele Alli. AFP
Talla

Alli bai samu jituwa da Mourinho ba  a lokacin da kocin dan kasar Portugal ke horar da Tottenham.

Sai dai yanzu dan wasan ya zama mai murza leda a kullayaumin a karkashin mai horarwa, However, Nuno Espirito Santo.

Dan shekara 25 din kasance cikin ‘yan wasan tsakiya da ake damawa da su a tsakiyar filin Tottenham a wannan zamani na Koch Nuno, kuma ya buga ilahirin wasannin gasar Firimiyar Ingila na wannan kaka tun da aka fara.

Alli ya shaida wa manema labarai cewa Mourinho yana da dabi’ar daukar lokaci yana nazari a kan abokan hamayya, maimakon ya mayar da hankali a kan abin da ya dace a yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.