Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Dortmund na bukatar Werner ya maye gurbin Haaland

Kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund, da ke wasa a gasar Bundesliga ta kasar Jamus ta ce za ta dauko dan wasan gaba na Chelsea, Timo Werner idan shahararren dan wasan gabanta Erling Haaland ya bar ta.

Star forward Erling Braut Haaland and his Norway teammates wore these t-shirts before a World Cup qualifying match
Star forward Erling Braut Haaland and his Norway teammates wore these t-shirts before a World Cup qualifying match JORGE GUERRERO AFP/File
Talla

An saka fam miliyan 68 a kwantiragin Haaland ga duk wanda yake bukatar raba dan shekara 21 din da Dortmunddaga kaka mai zuwa.

Ganin haka ne kungiyar ta kasar Jamus ta fara tattalin neman wanda zai maye gurbin dan wasan.

Werner, wanda ya koma Chelsea daga RB Leipzig a kakar da ta gabata, amma kuma ya fuskanci kalubale wajen saka kwallo a raga, yana daga cikin ‘yan wasa 4 da Dortmund ke neman maye gurbin Haaland da daya daga cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.