Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Hukumomin Barcelona na nazari kan sallamar Koeman

Hukumomin Barcelona na duba yiwuwar sallamar mai horar da ‘yan wasan kungiyar, Ronald Koeman, kamar yadda wasu kafofin yada labaran kasar Spain suka ruwaito.

Ronald Koeman, kocin Barcelona.
Ronald Koeman, kocin Barcelona. José Jordán AFP/Archivos
Talla

Duk da cewa akwai batun za a bai wa dan kasar Netherlands din Yuro miliyan 12 idan aka salame shi kafin ya karkare kwantiraginsa, wasu jami’an kungiyar na ganin korarsa din zai fi kwantar musu da hankali.

Koeman ya shiga karin matsin lamba ne bayan da  Barcelona ta kwashi kashinta a hannu 3-0 a gun Bayern Munich, a wasan farko na gasar zakarun nahiyar Turai da suka gwabza a daren Talata.

Yanzu rahotanni na cewa Ronald Koeman yana da wasani 3 ya ceto kansa daga sallama a kungiyar.

Shugaban Barcelona, Joan Laporta ya ji takaici matuka sakamakon rasin nasarar da kungiyar ta yi a hannun Bayern Munich, kuma gashi a gasar LaLiga za su hadu da Cadiz da Levante.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.