Isa ga babban shafi
Wasanni

Lewandowski ya lashe kyautar takalmin zinare na nahiyar Turai

Dan wasan gaba na Poland da ke taka leda a Bayern Munich mai doka gasar Bundesliga a Jamus Robert Lewandowski ya lashe kyautar takalmin zinaren nahiyar Turai na kakar wasan da ta gabata, bayan nasarar zura kwallaye 41.

Robert Lewandowski, dan wasan gaba na Bayern Munich.
Robert Lewandowski, dan wasan gaba na Bayern Munich. Marco Donato BAYERN MUNICH/AFP/File
Talla

Takalmin zinaren wanda bisa al’ada duk karshen kaka ake bayar da shi ga duk dan wasan da ya fi zura kwallo a gasannin lig din nahiyar ta turai, Lewandowski ya zama dan wasan lig din Jamus na biyu da ya taba lashe takalmin bayan Gerd Muller a shekarar 1971.

Da ya ke karbar takalmin Lewondowski dan Poland mai shekaru 33 ya ce ya sadaukar da shi ga ilahirin magoya bayansa.

Kwallayen na Lewandowski su ne mafi yawa da wani dan wasa ya zura tun bayan Cristiano Ronaldo a shekarar 2015 lokacin da ya zura kwallaye 48 yayin taka ledarsa a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.