Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Liverpool na shirin sayo Karim Adeyemi daga Salzburg

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta shiga jerin manyan kungiyoyin Turai da ke zawarcin dan wasan gaba na Jamus Karim Adeyemi.

Karim Adeyemi.
Karim Adeyemi. CHRISTOF STACHE AFP
Talla

Zuwa yanzu manyan kungiyoyin kwallon kafar Turai da suka kunshi Bayern Munich da Borussia Dortmund da kuma RB Leipzig su ne a sahun gaba da ke zawarcin Karim Adeyemi.

Matashin dan wasan mai shekaru 19 wanda ke taka leda da FC Salzburg, Club din da kansa ya sanar da cewa a shirye ya ke ya raba gari da shi a karshen wannan kaka.

Yanzu haka dai kungiyar ta Salzburg ta sanyawa Karim Adeyemi farashin yuro miliyan 25.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce kungiyar mai doka gasar Firimiya a shirye ta ke ta sayo Adeyemi.

Matashin dan wasan wanda tauraruwarsa ke haskawa zuwa yanzu ya zura kwallaye 8 cikin wasanni 10 da ya doka a wannan kaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.