Isa ga babban shafi
Wasanni

Real Madrid zata rasa damar sayen Haaland daga Dortmund

Akwai yiwuwar Real Madrid ba za ta samu sayen ɗan wasan gaba na Borussia Dortmund Erling Haaland ba saboda alamu sun nuna cewa zai koma Manchester City ko kuma Paris St-Germain. (AS - in Spanish)

Dan wasan Borussia Dortmund Erling Haaland
Dan wasan Borussia Dortmund Erling Haaland Ina Fassbender AFP
Talla

Borussia Dortmund na fushi sakamakon kocin Chelsea Thomas Tuchel ya fito fili ya bayyana ra'ayin kulob din na sayen Haaland. (Bild, via Mirror)

Barcelona na son ta sha gaban Real Madrid wajen sayen ɗan wasan gaban PSG da Faransa Kylian Mbappe inda kwantiragin ɗan wasan mai shekara 22 zai ƙare a kaka mai zuwa. (AS - in Spanish)

Manchester United da Chelsea na da ra'ayin ɗan wasan gaban na Norway mai shekara 21, wanda zai buƙaci albashin sama da fam miliyan 30 a shekara. (ESPN)

Everton na son sayen ɗan wasan tsakiyar Manchester United da Ingila Jesse Lingard mai shekara 28 a watan Janairu. (Football Insider)

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.