Isa ga babban shafi
Wasanni - Kwallon Kafa

Bayern Munich ta sha kashi irinsa na farko a shekaru 47

Bayern Munich ta sha mummunan kashi irinsa na farko tun shekara ta 1978, bayan da Borussia Monchengladbach ta yi mata yayyafin kwallaye 5-0 a gasar cin kofin Jamus.

Dan wasan Bayern Munich  Robert Lewandowski.
Dan wasan Bayern Munich Robert Lewandowski. REUTERS - ANDREAS GEBERT
Talla

Cikin minti biyu da saka wasan ne, Monchengladbach ta fara farke ragar Bayern Munich, sannan kafin minti 21, kungiyar ta zazzaga kwallaye uku.

Tuni jiga-jigan Bayern Munich suka bayyana kaduwarsau ta wannan rashin nasara, inda darektan wasanni na kungiyar, Hasan Salihamidzic ya ce, ko kadan ba su tabuka abin kirki ba.

Raban da a yi wa Bahyern Munich irin wannan zazzagar kwallayen tun shekaru 47 da suka gabata, lokacin da Fortna Dusseldorf ta doke su da ci 7-1 a gasar Bundesliga a wancan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.