Wani magoyin bayan Ingila zai yari na makwanni 10 saboda nuna wariya
Kotu a Ingila ta aike da wani magoyin bayan kwallon kafa gidan yari na makwanni 10 bayan samunsa da laifin nuna wariya ga ‘yan wasan kasar da suka kunshi Marcus Rashford da Jadon Sancho da kuma Bukayo Saka yayin wasan karshe na cin kofin yuro da ya gudana a filin wasa na Wembley da ke london.
Wallafawa ranar:
Wani faifan bidiyo mai dakika 18 ne ya gano Jonathon Best mai shekaru 52, na furta kalaman wariyar kan ‘yan wasan 3 bakar fata lokacin da suka gaza nasara a bugun fenaritin da ya hana Ingila nasara kan Italiya.
Rashin nasarar ta Rashford, Sancho da kuma Saka ne ya hana Ingila iya dage kofin na Euro wanda da shi ne zai zaman kofin wata babbar gasa karon farko da kasar za ta kai gida tun bayan kofin duniya a shekarar 1966 wato fiye da shekaru 50.
masana wasannin dai na ganin makamantan hukuncin za su taimaka wajen dakile wariyar da ‘yan wasa musamman bakaken fata ke fuskanta a fagen tamaula.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu