Isa ga babban shafi
Wasanni

Tsohon dan wasan United yayi barazanar shake wuyan kocin kungiyar

Tsohon kaftin din Manchester United Roy Keane, ya yi barazanar shake wuyan kocin kungiyar Ole Gunnar Solskjaer saboda cigaba da sanya dan wasansa dan asalin Brazil Fred a tawagarsa ta farko duk da rashin dacewar hakan.

Tsohon dan wasan Manchester United Roy Keane.
Tsohon dan wasan Manchester United Roy Keane. © Reuters/John Sibley
Talla

Keane da ya diga ayar tambaya game da makomar Solskjaer a United ya bayyana fusatar da yayi ne, a lokacin da yake zantawa da kafar watsa labaran wasanni ta Sky Sports inda ya ce da ace kocin zai matso kusa da shi a lokacin, to fa babu abinda zai hana ya shake wuyan shi.

Tsohon Kaftin din na Manchester United ya bayyana bacin ransa kan yadda  Manchester United ta sha kashi a hannun Manchester City da kwallaye 2-0 a ranar Asabar, makwanni biyu bayan da Liverpool ta lallasa su da kwallaye 5-0.

Yanzu haka Manchester United na matsayi na 6 a teburin Firimiya da maki 17, yayin da Manchester City ke matsayi na 2 da maki 23.

A sauran sakamakon wasu wasannin da akayi a gasar Firimiyar, Chelsea ta yi kunnen doki, wato 1-1 da kungiyar Burnley, amma kuma har yanzu itace ke matsayi na farko a tebur da maki 26, sai kuma Crystal Palace da ta doke Wolves da ci 2-0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.