Isa ga babban shafi
KWALLON-KAFA

Watford ta zazzagawa Manchester kwallaye 4 a Ingila

Kungiyar kwallon kafar Watford ta lallasa Manchester United da ci 4-1 a karawar da suka yi a gasar Firimiya ta Ingila, sakamakon dake ci gaba da nuna gazawar Manchester a gasar Firimiyar bana.

Manajan Manchester United Ole Gunnar Solskjaer
Manajan Manchester United Ole Gunnar Solskjaer Oli SCARFF AFP
Talla

Wannan sakamako na daga cikin koma bayan Manchester United ke fuskanta, abinda ke ci gaba da nuna ko kwanton akan makomar mai horar da kungiyar Ole Gunnar Solskjaer. 

King ya fara jefawa Watford kwallo a minti 28 da fara wasan, yayin da Sarr ya jefa ta biyu bayan ya barar da bugun fenariti har sau biyu, inda aka tafi hutun rabin lokaci Watford na da ci 2-0.

Yan wasan Manchester Cristiano Ronaldo da Wan Bissaka
Yan wasan Manchester Cristiano Ronaldo da Wan Bissaka Marco BERTORELLO AFP

Dawowa daga hutun ‘dan wasan Manchester van de Beek ya farke ci guda a minti 50, yayin da alkalin wasa ya kori kaftin din Manchester United Maguire saboda aikata keta a minti 69.

Korar Maguire ta baiwa Watford karfi inda suka jefa kwallaye biyu a mintina 92 da minti 96 na wasan, nasarar da ta fitar su daga kasan teburin gasar.

Wannan ba karamar nasara bace ga sabon manajan kungiyar Watford Claudio Ranieri.

 N'Golo Kante lokacin da ya jefawa Chelsea kwallo a karawar su da Leicester
N'Golo Kante lokacin da ya jefawa Chelsea kwallo a karawar su da Leicester © Ben STANSALL AFP

Kafin karawar Manchester, kungiyar Chelsea ta lallasa Leicester da ci 3-0, Aston Villa ta samu nasara akan Brighton da ci 2-0, yayin da karawa tsakanin Burnley da Crystal Palace aka tashi 3-3.

Kungiyar Newcastle ta tashi 3-3 da kungiyar Brentford, yayin da Norwich ta doke Southampton da ci 2-1, sai kuam Wolves da ta samu nasara akan West Ham da ci 1-0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.